Friday, August 31, 2007

Mun gane masu cutarmu,

Shugabanni ne macutar mu,

Sune masu zanbar mu,

Mun san basu kaunar mu,

Sun kwashe dukiyoyin mu,

Sun kaita a can ga turawa.


Masu mulki ne na zalumci,

Mulkin Rashawa da cin hanci,

Mulkin shirme da lalaci,

Ba sa Sharia ta adalci,

A Mulkin nasu b a yanci,

Wai koyi suka yi da Turawa.


Talauci da sunka kago shi,

A kan talaka su dora shi,

Suka sa tsari na kara shi,

Ilimi suka fara rusa shi,

Su kasa nakasa a hanyar shi,

‘Ya'yansu su kai wa Turawa.


Dubi dai maganar rowan shan mu, '


Da harkar lafiya tamu,


Baban maganar tsaro namu,


Na duk fadin kasa tamu,


Sun ki jin gunji na kukanmu


Don suna Hulda da Turawa.




Yanzu dai mu bamu zaban ku,


A dama ma munki zaban ku,


Kun murde da karfin ku,


Da yanda da sojan ku,


Da hukuman nan ta zaben ku,


Da munafinci na Turawa.




Mu kam yanzu mun gane,


Ku dai masu son kai ne,


Daga ku sai naku sai wane,


Talakawa yanzu mun gane,


Mun gane ku barayi ne,


Ku saci kukai wa Turawa.




Dubi mannyan kamfanonin mu,


Wadanda suke kasa ta mu,


A yau sun barfa hannun mu,


Sun kwace wa kasa ta mu,


Sun sauya dukka jarin mu,


Ga junansu da Turawa.




Jama'a lallai kusan wannan,


A kwai zabe fa kwanannan,


Ku bude idanku kan wannan,


Ku zabo adilai hakanan,


Masoya naku don hakanan,


Marasa gama kai da Turawa.




A ran zabe ku zabe su,


Kun gane su kun san su,


Masu kaunar ku ku zabe su,


Jama'a nasonsu kun sansu,


Don Allah ne yake son sonsu,


Don nufin su na taimakon kowa.




Yau jama'ar mu sun waye,


Kowa yau kansa ya waye,


Ya san yadda ake fa tawaye,


Mu tsaya don kammu ya waye,


Idan kuriar mu sun tauye,


Mu taru mu casa dan kowa.




Idan muka kyale yan zulmu,


Makiya namu da "ya'yan mu,


Muka kyale har su cuce mu,


Lallai mu sabi Allan mu,


Don mun kyale da yan zulmu,


Marasa jin tausayin kowa.




Alhamdulillahi

No comments: